(ABNA24.com) Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da janye tallafin da kasarsa ke baiwa hukumar lafiya ta duniya (WHO), bisa zarginta da karya da kumbiya kumbiya wajen tafiyar da al’amarin annobar coronavirus.
M.Trump, ya ce duniya ta samu sakwannin karya masu yawa game da bayanan yadda cutar coronavirus ke yaduwa da kuma yadda take kisa.
A don haka ya ce ya dakatar da tallafin da kasarsa ke baiwa hukumar, a daidai lokacin da ake gudanar da bincike kan yadda WHO din ta boye bayanai game da yaduwar annobar.
Amurka dai na baiwa hukumar ta WHO, tallafin dala miliyan 400 zuwa 500 a ko wacce shakera inji Trump, a daidai lokacin da China ke bada miliyan 40 ko kasa da hakan ma, wanda kuma a cewarsa dole ne kasar ta nemi bahasi game da hakan.
Matakin na Trump, bai zo da mamaki ba, domin kuwa yana zuwa ne a daidai lokacin da adadin mutanen da cutar ta covid-19 ke kashewa a Amurka ke dada karuwa fiye da ko ina a duniya, inda alkalumman baya baya nan ke cewa mutum sama da 2200 ne cutar ta kashe a kasa da sa’o’I 24.
Game da matakin na Amurka babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya ce rage tallafin bai dace da wannan lokaci da ake ciki ba.
/1289
16 Afirilu 2020 - 04:59
Lambar labari: 1026289
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da janye tallafin da kasarsa ke baiwa hukumar lafiya ta duniya (WHO), bisa zarginta da karya da kumbiya kumbiya wajen tafiyar da al’amarin annobar coronavirus.